Tuesday, October 9, 2012

Easily Upload Your Images To Myspace
Free Music HADEJIA A YAU!
SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya
yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi
da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne
shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana
tsakaninsu dashi Buhari.

Kamar SARKIN AREWA TATA
GANA (GINSAU MAI KINA BAWO) DA KUMA SARKIN
YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI
SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!
SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da
shekara Goma sha Hudu. Kuma manyan fadawan
Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi
yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram
Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a
Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim
mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki
amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba.


Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa!
Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka
cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo.
Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki
sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya
koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana
kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka
sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma
saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin
Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne!
Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin
Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka
fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagaram
yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu
tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina
mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki
dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu
san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma
Damagaram.

Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka
ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba.
Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da
ruwa a kusa dasu. SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne
mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko
Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan
Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa.


Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo
ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia
Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN
BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a
shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.
HADEJIA A YAU

HADEJIA A YAU!: KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA

HADEJIA A YAU!: KASAR HADEJIA DA KABILUN CIKINTA: HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar 1,HAUSAWA 2, ABORAWA (FULANI) 3, MANGAW...

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...