Saturday, May 30, 2015

AN KAMMALA TARON KADDAMAR DA KUNGIYAR MOVEMENT FOR THE RESTORATION OF NORTHERN NIGERIAN DIGINITY.


A Hadejia ta jihar jigawa ne aka kaddamar da wannan kungiya, a karkashin Jagorancin Dr. Aliyu M. Muri. na jami'ar umaru musa 'yar'adua dake katsina, taron ya sami halartar shugabanni da Membobi na kungiyar Muryar Talaka dake jihar jigawa, kuma an gabatar da Jawabai masu muhimmanci domin ganin an Taimakawa Gen. Buhari don ya Aiwatar da mulkinsa cikin Nasara. Da yake nasa Jawabin Dr. Aliyu Muri ya tabo fannoni da dama wanda jama'a zasu taimakawa kansu wajen zaben wanda zai wakilcesu a kowane mataki na Gwamnati, kuma yayi kira ga mahalarta taron dasu hada kai da hukumomin gwamnati domin samun nasara a duk harkokinsu na kungiya. Shima a nasa jawabin Comrade Bishir Dauda ya ja hankalin mahalarta taron wajen hada kai da hukumomi irin su NOA, EFCC, ICPC Da sauransu. Cikakken Rahoto zaizo daga Baya.

ZA'A KAI RUWA RANA TSAKANIN TSHOHON GWAMNAN JIGAWA SULE DA SABUWAR GWAMNATIN BADARU ABUBAKAR.


Alamu na nuna cewa a jahar jigawa za'akai Ruwa Rana Tsakanin tshohon Gwamnan jahar Sule lamido da kuma sabon Gwamna Alh Abubakar Talamiz Inda yanzu haka Sabon Gwamnan Alh Abubakar Badaru Ya musanta cewar: Tsahon Gwamnan Alh Sule lamido Sam Sam ba Biliyon Goma sha hudu 14n ya barmasa bashi ba ya ce kudin ya Nin ninka hakan Inda ya ce yanzu haka jahar ta jigawa ana binta kudaden da suka kama har kimanin Biliyon Dari da sha hudu 114b akasin abinda tsohon Gwamnan ya fadi a baya Dan haka sabon Gwamnan yayi alwashin yin bincike akan yadda aka bayar da duk basusukan. Shi kuma a nasa bangaren Shugaban Jam'iyar Adawa ta PDP a jahar Alh muhammed Mahamud Ku'it ya danganta wadannan maganganu da yan Jam'iyar ta APC sukeyi da cewar Jahilci ne ko kuma rashin sanin kwata kwata tsari na iya mulki. Sule lamido dai ya shafe shekaru takwas yana mulki a jihar jigawa, inda kuma yaci karensa babu babbaka sakamakon rashin 'yan Adawar da zasu taka masa birki game da yanda yake mulkin Jigawa. A satin da ya gabata ne Sule Lamidon ya tafi wani dogon hutu, inda ya bar Jihar a hannun sakataren Gwamnatin Jigawar wanda kuma shine ya mika mulki ga sabuwar Gwamnati, tuni dai masu sharhi suka danganta wancan hutu na Tsohon gwamnan da cewa wani salo ne na Tserewa sakamakon dinbin bashin da ya barwa Jihar. Abin jira a gani dai shine ko Sule Lamido zai dawo da wadannan kudade? Kokuma sai an kwatosu da karfi.

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...