


A Hadejia ta jihar jigawa ne aka kaddamar da wannan kungiya, a karkashin Jagorancin Dr. Aliyu M. Muri. na jami'ar umaru musa 'yar'adua dake katsina, taron ya sami halartar shugabanni da Membobi na kungiyar Muryar Talaka dake jihar
jigawa, kuma an gabatar da Jawabai masu muhimmanci domin ganin an Taimakawa Gen. Buhari don ya Aiwatar da mulkinsa cikin Nasara.
Da yake nasa Jawabin Dr. Aliyu Muri ya tabo fannoni da dama wanda jama'a zasu taimakawa kansu wajen zaben wanda zai wakilcesu a kowane mataki na Gwamnati, kuma yayi kira ga mahalarta taron dasu hada kai da hukumomin gwamnati domin samun nasara a duk harkokinsu na kungiya.
Shima a nasa jawabin Comrade Bishir Dauda ya ja hankalin mahalarta taron wajen hada kai da hukumomi irin su NOA, EFCC, ICPC Da sauransu. Cikakken Rahoto zaizo daga Baya.
No comments:
Post a Comment
KA RUBUTA RA'AYINKA!