Thursday, June 14, 2012

JIHAR BORNO

MANYAN BORNO SUN ROKI DA A KAWO KARSHEN RIKICIN BOKO HARAM HADEJIA A YAU! Al'ummar Jihar Borno dake Arewacin Nigeria sun Roki 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunna lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram da su Amince a tattauna dasu da Gwamnati domin a kawo karshen Hare harenda yake janyo Rasa rayuka da gidaje. A wata fira da yayi da 'yan jarida a Maiduguri Dr. shettima Ali Munguno ya bayyana rikicin boko haram a matsayin rikici ne wanda ya janyo Asarar rayukan Al'umma da gidaje, kuma ya janyo Rashin aikin yi ga Al'umma. Ya bayyana cewa mutane basu kwanciyar hankalin da zasu tafiyar da rayuwarsu a tsinake, ko harkokinsu na yau da kullum.uma ya bayyana cewa Jama'a basu samun salloli Biyar a cikin Jam'i saboda fargabar abinda zai kasance,Saidai mutum yayi sallarsa a cikin gidansa saboda rashin samun nutsuwa. Dr.Ali Munguno ya kara da cewa yana rokonsu da su Amince a tattauna dasu domin a kawo karshen Asarar rayuka da ake. yace a matsayinsu na 'yan kasa suna da ikon rayuwa a jikin mutane ba tare da tsangwama ba. yace duka mu da su kasarmu ce, bamu da wata kasar da tafi wannan. kuma ya kara da cewa Gwamnatin tarayya tare da gwamnatin Jiha a hada hannu wajen tattaunawar domin a kawo karshen wannan Al'amari. http:// Isabohadejia.blogspot.com/

TARIHIN SARKI HARU BUBBA

TARIHIN SARKIN HADEJIA HARU BUBBA Sarkin Hadeji Haru bubba shine Mahaifin Sarkin Hadejia Muhammadu mai Shahada, wanda a zamaninsa Turawa sukaci Hadejia da yaki. Sarki Haru bubba Malami ne kuma mutum ne mai son zaman lafiya, kuma shine ya gina Masallacin juma'a Na Hadejia. Kuma a zamaninsa Gumel sukayi yaki da Hadejia, wato lokacin sarkin Gumel Abdu jatau. Sarkin Gumel ya aikowa Sarkin Hadejia zai wuce ta kasarsa wato ta kudu a gayawa Talakawa kada su tsorata bazai taba kowa ba. To amma koda yazo wucewa sai ya saba Alkawari don yana sawa ana debe kayan talakawan ana kaiwa Gumel. Koda Sarkin Hadejia ya samu labari sai yasa akayi sirdi aka fita, a wannan yakin aka kashe sarkin Gumel Abdu jatau. Galadiman Hadejia yakuba shine ya sareshi. Dama sarkin Gumel yayi mafarki bazai koma gida ba. Sai ya fadawa kaninsa Abubakar in ya mutu to a kaishi Gumel ayi masa jana'iza, kuma hakan akayi. Kuma a zamanin Sarkin Hadejia Haru ne Dansa Muhammadu Yayi yaki da Maguzawan Mada Rumfa ta Sokoto, inda sarkin musulmi ya masa sarautar Sarkin yakin Sarkin Musulmi. Kafin ya Zama Sarkin Hadejia. Allah yaji kansu.

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...