Thursday, June 4, 2015

YANDA DOLE TASA 'YAN GUDUN HIJIRA BARA A KASAR HADEJIA.

Tun daga lokacin da garin Allah zai waye har zuwa faduwar rana ka dinga cin karo kenan da Mata da Kananan yara suna yin bara ko naiman taimako, musamman a Arewa maso gabashin jihar Jigawa. Wadannan bayin Allah sun tsinci kansu a wannan hali ne sakamakon rikicin Boko Haram da ya Addabi Jihohin Borno da Yobe, dole wasu suka baro gidajensu domin neman tsira daga wannan Bala'i. Wasu kuma an kashe musu Mazajensu an kone gidajensu basu da wata sauran Dabara sai dai suyi bara domin su ciyar da kansu da yaransu.

Sakamakon Makwaftaka dake tsakaninsu da Jihar Jigawa, musamman Kasar Hadejia, bazakayi minti goma kana zaune ba sai kaci karo da wadannan bayin Allah suna cewa A taimaka mana da sadaka, mu 'yan gudun hijira ne..

A jihar Jigawa dai wadannan 'yan gudun hijira gwamnatin baya bata taba tallafa musu da komai ba, ko gida ko abinci ko sutura, sakamakon Kabilanci da yayi Tasiri a zuciyar tsohon gwamnan, wanda bincike ya nuna cewa abinda yasa ya nuna halin ko in kula ga wadannan mutane shine.. Suna zaune ne a wani bangaren Jihar ta Jigawa wanda kuma shi a zuciyarsa abin bai shafeshi ba.

Abin jira a gani dai shine... Ko sabuwar Gwamnatin Jigawa zata waiwaici wadannan bayin Allah? Ganin cewa wasu da yawa babu abinda zasu koma suyi a garuruwansu, sakamakon Kone musu gidaje da dukiyoyi da kashe musu 'yan-uwa da akayi. Allah ya baiwa sabuwar gwamnati ikon taimakawa......

http://bit.ly/K2WOg4

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...