Monday, June 1, 2015

EFCC TA CAFKE MA'AIKATAN BUBBAN BANKI SU SHIDA.


DAGA JARIDAR LEADERSHIP. Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nijeriya -EFCC za ta gurfanar da wasu manyan jami’an babban bankin kasar gaban kuliya bisa zargin yin zambar kusan naira biliyan takwas. Hukumar EFCC ta ce manyan jami’an bankin na CBN su shida tare da wasu jami’an bankunan ‘yan kasuwa na kasar su 16 sun hada baki wajen yin zambar wadannan makudan kudaden ta hanyar sauya adadin wasu tsofaffin kudi da suke kula da su.

A cikin wata sanarwa, kakakin EFCC Wilson Owujaren ya ce za a gurfanar da wadannan mutanen su 22 gaban babbar kotun tarayya da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo. A cewar EFCC jami’an na bankin CBN sun hada da Patience Okoro Eye, Afolabi Olufemi, Kolawole Babalola, Olaniran Muniru Adeola, Fatai Yusuf Adekunle da kuma Ilori Adekunle Sunday. Mazambatan suna yin wata badakala ce ta tsofaffi da kuma yagaggun kudade a jihohi da dama na kasar.

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...