Thursday, February 25, 2016

KWAMISHINAN LAFIYA YA KAI ZIYARAR BAZATA ASIBITIN HADEJIA...




A Yau kwamishinan lafiya na jahar Jigawa ya Kawo Ziyarar aiki a garin Hadejia, inda yaje wurin da gwamnatin Jihar jigawa ta ware domin gina sabuwar makarantar koyon aikin jinya da Ingozoma a garin Hadejia (school of nurse and midwifery) A lokacin Ziyarar kwamishinan ya karbi gudunmawar dakin karatu wadda wata kungiya mai suna women4health ta Gina kuma ta bawa gwamnatin jahar jigawa domin samun nasarar gudanar da karatu a wannan makaranta kamar yadda wannan Gwamnati ta Kudirta zatayi.

Taron wadda ya samu halartar shi kansa kwamishinan lafiya Dr. Abba Zakari da kuma rakiyar Bubban sakatare na ma'aikatar lafiya ta jihar Jigawa, sai wakilin maimartaba Sarkin Hadejia, Maigirma Wazirin hadejia Alh Hashim Amar, sai shugaban wannan kungiya ta women for health reshen Jihar Jigawa Mr. Robert bature da abokan aikinsa da 'yan kungiyar mata, da kuma shugaban kwamatin lafiya na majalisar dokoki na jihar jigawa, Dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Garki Alhaji Lawan Garba, da membobin kwamatinsa da wakilan kungiyar Hadejia ina mafita Babangida kakabori da mu'azu Abu Juwairiyya da Muhammad B Dan Iya, sai mu'azu Hamza Abbas da wakilan ma'aikatar mata ta jiha da 'yan rakiyar kwamishinan lafiya na Jihar Jigawa.

Bayan karbar wannan gudunmawa dai kwamishinan ya yabawa shugabannin wannan kungiya bisa namijin kokarin da sukayi na wannan aiki, sannan yayi kira garesu da suci gaba da taimakawa gwamnati da irin wannan aiki na alkairi domin ganin an hada karfi da karfe an ciyar da Jihar Jigawa gaba. Daga nan kwamishinan yakai Ziyarar gani da ido wurin da za'ayi Asibitin kwararru wato Specialist Hospital da gwamnatin Jihar Jigawa zatayi, sannan yakai Ziyarar bazata Bubbar Asibitin Hadejia.

RAHOTO DAGA.... Babangida Chairman Kakabori.

posted from Bloggeroid

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...