Saturday, September 8, 2012

YAKIN KAFUR KO GAMON KAFUR


HADEJIA A YAU!
Bayan da aka kare Yakin Takoko inda aka kashe Sarkin Hadejia Ahmadu, Daular sokoto dai sunki yarda da Buhari a Matsayin Sarkin Hadejia. Sarkin Musulmi Alu Bubba sai ya gayyaci duk sarakunan dake Karkashin Daular sokoto da su hadu su yaki Buhari. Ko a kamashi da rai ko a kashe shi. Wannan kuwa ta faru ne a shekarar (1853). An hada wannan rundunar yakin ne karkashin Jagorancin Galadiman Kano Abdullahi maje Karofi kafin ya zama Sarkin Kano. An gayyaci mayaka a Garuruwa daban daban kamar Kano,zamfara,Bauchi,Katagum,Misau,zaria da sauran garuruwan Daular Sokoto. Masana tarihi sunce an tara mutum A kalla Dubu Ashirin (20,000) Abdullahi Maje Karofi ya Umarci Sarkin Miga da ya zame musu Jagoran Tafiya, ganin cewa ya fisu sanin Kasar Hadejia saboda Iyakarsu daya. Koda suka shirya sai aka Umarcesu da su shiga Hadejia ta Kudu Maso Yamma, wato kar su shiga kai tsaye ta yamma. Akan Hanyarsu ta zuwa Hadejia ne Sai suka Yada Zango a Kafur, kusa da Hadejia. Domin su kwana da safe su shiga Hadejia su Yaki Sarki Buhari. Sai dai da zuwansu Kafur Buhari ya samu Labari, Ance wani makiyayi ne yana kiwo ya Gansu, kuma Har ya bar gurin baiga Iyakarsu ba. Sai ya rugo ya sanarda Sarki Buhari Abinda ya gani. Sai Buhari ya Umarci Mayakansa cewa "Tunda ance Basu da iyaka kuma ga Magariba ta shigo, mu shirya muje mu shiga cikinsu ba tare da sun ganemu ba" hakan sukayi yace Duk Lokacinda sukaji Dan fatima ya Buga Ganga to su fara Bugun mayaka. Haka akayi Mayakan Buhari suka shimmace su suka shiga cikinsu ba tare da sun gane ba,Saboda Garuruwa da dama ne suka Hadu. Ance wasu mayakan nasu Dauresu akayi wai dan kar su shiga Hadejia kafin Gari ya waye. Ashe Ajali ne ya dauresu.
Koda Sarkin Hadejia Buhari yayi shirinsa yayi Addu'ah sai ya Daga Kai sama. Sai Dan fatima ya zuba Kirari (Fasa maza dan Sambo, Garba Bakin Tandu da Man Madaci, wanda ake jira yazo, fasa Maza gagara gasa, sai ya buga Gangar yaki). Anan Mayakan Hadejia suka fara bugun mayakan Daular Sokoto suna kashewa. Wadansu duk suka razana suka fita a guje kowa yana kokarin ya ceci Ransa. Wadanda aka dauresu dan kar su shiga Hadejia da wuri, duk anan aka kashesu. Sauran kuwa suka zubar Makamansu suka Gudu. Dawakai suka Razana, su kuwa mayakan Hadejia Suna bi suna kashewa suna kama Bayi.

ANNABI MUSA KALAMULLAHI. DAGA IDRIS M. EDDY


ANNABI MUSA(A)
Annabin Allah ne da ya ke magana da Allah
wajen karban sako ba tare da mala'ika a
tsakani ba. Annabi Musa ne Annabin da ya fi
kowanne Annabi shan wahalar isar da
manzanci.
* Na farko ya yi gwagwarmayar neman aure a
Madayyana a gidan Annabi shu'aib
* Na 2 ya yi gwagwarmaya da mutumin da a
tarihi shi kadai ya taba da'awar rububiyya da
uluhiyya. Kuma Allah ya kirashi da gwani
wajen azabtar da mutane. Kuma mutanen sa
na matukar biyayya gare shi kan da'awar sa
ta Allantaka.
* Na 3 ya kai ruwa rana da attajirin da ba a
taba yin irinsa ba a tarihin Duniya. Bayan
wadata ya bijrewa Allah kuma ya sami
tumasawa da jama'ar gari su ka daure mashi
gindi.
* Na 4 ya yi fama da mutumin da a tarihi shi
kadai mala'ika ya rena kuma ya kafirce ya ke
neman kafirtar da jama'ar Annabi
Musa.Samiree ya samar da abin bautar da ba
Allah ba bayan Annabi Musa ya tafi karbo
sakon Allah. Mutane Annabi Musa gaba daya
su ka canja addini sai yan kadan su ka rage.
* Na 5 Annabi Musa ya sha fama wajen
karantar wasu darussa na rayuwa daga
wajen Hadhiru. Bawan Allah n da aka tura
Annabi Musa musamman ya je ya dauko
darasi a wurin shi.
* Na 6 sai famar sa da ta fi kowacce wahala
wacce kuma ita Allah ya fi yawan maimaitawa
a kur'ani kuma ita Allah ke kafawa kafirai
hujja duk lokacin da su ke neman tadawa
wani Annabi hankali kan sai ya kawo masu
hujja,
- Ana sauko masu abinci daga aljanna amma
su ka ce ya ishe su su nomawa za su na yi.
- sun yi laifi ance su nemi gafara da wata
kalma sai su ka canja wata. Kamar ace ku ce
'Gafara' sai su ka ce 'Ga fura'.
- sun ce su sun fasa imanin ma har sai sun ga
Allah da idon su . Aka kai su su ka ji sauti
magana daga Allah suka ce ba su amince ba .
Sai da su ka ga wani haske daga Allah su ka
fadi matatu. Allah ya rayar da su.
- sun tambayi Annabi musa me ya kamata ayi.
Allah ya sanar da shi a yanka saniya. Amma sai
su ka ce wacce iri? Ya fadi irin su ka ce wacce
kala? Sai aka fada musu abin da sai da suka
mika wuya don dole.
- An umarce su da sujjada sun ki sai da aka
sauko da dutse zai fado masu.
- wadannan su ne masu imani daga cikin
mutanensa, amma ko Allah za su kira sai su ce
da Annabi musa ka roka mana Allah nka ya
mana kaza.
* Na 7 Annabi Musa famarsa ta karshe da
mutanesa ce lokacin da Allah ya umarcesu su
shiga gari na karshe da ya rage na al'ummar
Adawa a doron Duniya. Su yaQe su duk da
girmansu su shiga garin su zauna ya zama
nasu mai makon wannan yawo da su ke. Da
yan leken asiri ( su Yusha'u) su ka dawo su ka
bayyana yadda girman Adawa ya ke sai su ka
ce to mu mun tsaya anan ya Musa sai dai in
ku je ku yi yakin da kai da Allah nnaka.
Wannan dalili ya jawo masu dimuwa shekara
40 ba su san inda su ke ba. A wannan
dimuwa Annabi Musa da Annabi Haroon da
dattawa da yawa daga cikinsu su ka rasu.
Annabi (s) ya yi addu'a kan Allah Sakawa
Annabi Musa da alkhairi kan hakuri da ya yi
da cutarwar da jama'arsa su ka masa .
Annabi Musa ne Annabi daya tilo da aka bashi
Annabta kuma ya rokawa dan uwansa
Annabta. Annabi Musa ne aka ambaci sunansa
har x 136 a ckin kur'ani. Annabi Musa suruki
ne na Annabi Shu'aibu(A)
Allah saka wa Hasiya matar Fir'auna da
alkhairi da ta sadaukar da rayuwarta don
amsa da daukaka kiran Annabi Musa.
Allah saka ma Yusha'u da alkhairi saboda
biyayya da bada kwarin gwiwa ga Annabi
Musa da jagorantar rundunar da Annabi Musa
ya mutu ya bari ya je ya cinye garin da yaki su
ka maye garin kamar yadda Allah ya
alkawarta.
Annabi Musa ya taimakawa al'ummar
musulmi da shawartar Annabi(s) da ya nemo
mana saukin sallah daga 50 ta dawo 5 . Allah
kara daraja da gafara ga Annabi Musa(A.s.)

Annabi Musa ya kafa hujja ga kiristoci. Cikin
tsohon alkawari ya na cewa Annabin da zai
zo akarshe kamar ni ya ke, ni ma kamar shi na
ke.
Kamanninsu.
.. Suna da uwa da uba.
.. Sun yi hijra
.. Garinsu da ganuwa
.. Sun yi yaki
.. Sun yi aure
.. Sun haifi yaya
ko nan kamannin su ka tsaya sun wadatar da
cewa a cikin Bible hujja ta tabbata daga
Annabi Musa Annabi Isa ba shine Annabin
karshe ba.

FADAKARWA DAGA MASALLACIN FANTAI. DAGA IDRIS BAFFA


Assalamu Alaikum. Ya yan uwa musulmai, hakika malam husaini
baban(nai‘bin masallacin usman dan fodio dake cikin babbar
sikandiren gwabnati(fantai hadejia) yaja hankalinmu a yayin dake
gabatar da kdabarsa ta sallar juma‘a.malam yayi bayani akan
mahimmacin(ihsa n)kyautatawa, a inda yabukaci mutani su dage
wajen taimakawa masu karamin karfi da kuma taimakawa addinin
musulinci ta bangaruri dabandaban.haki ka malam ya janyo ayuyi
daga AL-QUR‘ANI MAI GIRMA DA KUMA HADISAN MANZO
(SAW)ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YAFADA A CIKIN SURA TA
3, AYA TA 91.(Baza ku sami kyautatawaba, sai kun ciyar daga abin
da kukeso. Kuma abin da kuka ciyar, komene ne, to lalle ne ALLAH
gare shi masani ne). Yazo cikin hadisi, wata rana MANZO(SAW) tare
da sahabbansa masu daraja za‘atafi yaki, a wannan lokaci ana cikin
tsanani ga rana, ga sahara ga ba dawakan fita, wasu daga cikin
sahabbai irensu sayyadna ABUBAKAR SIDDIK, UMAR BN KHADDAB
da sauran su. Sun fitar da dukiyoyinsu ba don komaiba sa don
samun rabo mai girma a gobe. Da fatan wannan kudba ta malam
jatayi tasiri cikin zikantamu amin.

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...