Friday, May 29, 2015

AN RANTSAR DA SABON GWAMNAN JIHAR JIGAWA. Daga Garba Tela Hadejia.


SARDAUNA/SHATIMA SUN KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI.... Daga Garba Tela Hadejia. A yau juma'a 29-5-2015 ne sabon zababben gwamnan jihar Jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar (Sardaunan Ringim), da kuma mataimakinsa Barr. Ibrahim Hassan Hadejia (Shatiman Hadejia) suka karbi rantsuwar kama aiki gadan-gadan, domin hidima ga Al-ummar Jihar Jigawa. Da farko, an umarci Chief Jojin Jiha domin ya bude taro da Addu'a, Daga bisani, aka bukaci babban jigo a jam'iyyar ta (APC) wato Hon. Farouk Adamu Aliyu Birnin-Kudu ya gabatar da jawabinsa. Daga bisani aka sake bukatar Chief Jojin ya rantsar da mataimakin gwamna. Daganan kuma sai ya sake dawowa a karo na uku ya rantsar da gwamna.Bayan haka kuma aka Umarci mawaki Lawan Gujungu ya dan jijjiga-filin taro na wasu 'yan dakikoki kadan cikin sabuwar wakar da ya yiwa sabon gwamna. Daga bisani anso gabatar da Faretin girmamawa ga sabon Gwamna wanda jami'an tsaro za su gudanar amma hakan bata samuba sakamakon dandazon taron Al-umma masoya da suka cika filin wannan taro. Daganan kuma Sabon gwamna ya gabatar da jawabinsa ga Al-umma cikin harshen turanci bisa tanadin doka. A'karshe kuma, an gudanar da Addu'ar rufewa. Gami da 'yan shagulgula da jawabai kafin bajewa daga wannan filin taro. An gudanar da taron a filin taro na Malam Aminu Kano Tiraiangle dake birnin Jiha Dutse. Taron ya samu halattar dubban Al-umma daga sassa daban-daban na wannan Jiha. Sabon Gwamna da mataimakinsa, sunci alwashin gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci a wannan Jiha ta Jigawa. Insha Allah! A takaice, abin kenan da ya gudana ya yin rantsar da sabon zababben gwamnan Jihar Jigawa da mataimakinsa a birnin Jihar Jigawa Dutse. Muna kara godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana mai cike da farin ciki da tarihi a garemu. Allah ya taimakesu ya 'karfafesu akan dai-dai. Garba Tela Hadejia.

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...