

Alamu na nuna cewa a jahar jigawa za'akai Ruwa Rana
Tsakanin tshohon Gwamnan jahar Sule lamido
da kuma sabon Gwamna Alh Abubakar Talamiz Inda yanzu haka Sabon Gwamnan Alh Abubakar
Badaru Ya musanta cewar:
Tsahon Gwamnan Alh Sule lamido Sam Sam ba Biliyon Goma sha hudu 14n ya barmasa bashi
ba ya ce kudin ya Nin ninka hakan Inda ya ce yanzu haka jahar ta jigawa ana binta
kudaden da suka kama har kimanin Biliyon Dari
da sha hudu 114b akasin abinda tsohon Gwamnan ya fadi a baya
Dan haka sabon Gwamnan yayi alwashin yin
bincike akan yadda aka bayar da duk basusukan.
Shi kuma a nasa bangaren Shugaban Jam'iyar
Adawa ta PDP a jahar Alh muhammed Mahamud Ku'it ya danganta wadannan
maganganu da yan Jam'iyar ta APC sukeyi da
cewar Jahilci ne ko kuma rashin sanin kwata kwata tsari na iya mulki. Sule lamido dai ya shafe shekaru takwas yana mulki a jihar jigawa, inda kuma yaci karensa babu babbaka sakamakon rashin 'yan Adawar da zasu taka masa birki game da yanda yake mulkin Jigawa.
A satin da ya gabata ne Sule Lamidon ya tafi wani dogon hutu, inda ya bar Jihar a hannun sakataren Gwamnatin Jigawar wanda kuma shine ya mika mulki ga sabuwar Gwamnati, tuni dai masu sharhi suka danganta wancan hutu na Tsohon gwamnan da cewa wani salo ne na Tserewa sakamakon dinbin bashin da ya barwa Jihar. Abin jira a gani dai shine ko Sule Lamido zai dawo da wadannan kudade? Kokuma sai an kwatosu da karfi.
No comments:
Post a Comment
KA RUBUTA RA'AYINKA!