Saturday, September 8, 2012

YAKIN KAFUR KO GAMON KAFUR


HADEJIA A YAU!
Bayan da aka kare Yakin Takoko inda aka kashe Sarkin Hadejia Ahmadu, Daular sokoto dai sunki yarda da Buhari a Matsayin Sarkin Hadejia. Sarkin Musulmi Alu Bubba sai ya gayyaci duk sarakunan dake Karkashin Daular sokoto da su hadu su yaki Buhari. Ko a kamashi da rai ko a kashe shi. Wannan kuwa ta faru ne a shekarar (1853). An hada wannan rundunar yakin ne karkashin Jagorancin Galadiman Kano Abdullahi maje Karofi kafin ya zama Sarkin Kano. An gayyaci mayaka a Garuruwa daban daban kamar Kano,zamfara,Bauchi,Katagum,Misau,zaria da sauran garuruwan Daular Sokoto. Masana tarihi sunce an tara mutum A kalla Dubu Ashirin (20,000) Abdullahi Maje Karofi ya Umarci Sarkin Miga da ya zame musu Jagoran Tafiya, ganin cewa ya fisu sanin Kasar Hadejia saboda Iyakarsu daya. Koda suka shirya sai aka Umarcesu da su shiga Hadejia ta Kudu Maso Yamma, wato kar su shiga kai tsaye ta yamma. Akan Hanyarsu ta zuwa Hadejia ne Sai suka Yada Zango a Kafur, kusa da Hadejia. Domin su kwana da safe su shiga Hadejia su Yaki Sarki Buhari. Sai dai da zuwansu Kafur Buhari ya samu Labari, Ance wani makiyayi ne yana kiwo ya Gansu, kuma Har ya bar gurin baiga Iyakarsu ba. Sai ya rugo ya sanarda Sarki Buhari Abinda ya gani. Sai Buhari ya Umarci Mayakansa cewa "Tunda ance Basu da iyaka kuma ga Magariba ta shigo, mu shirya muje mu shiga cikinsu ba tare da sun ganemu ba" hakan sukayi yace Duk Lokacinda sukaji Dan fatima ya Buga Ganga to su fara Bugun mayaka. Haka akayi Mayakan Buhari suka shimmace su suka shiga cikinsu ba tare da sun gane ba,Saboda Garuruwa da dama ne suka Hadu. Ance wasu mayakan nasu Dauresu akayi wai dan kar su shiga Hadejia kafin Gari ya waye. Ashe Ajali ne ya dauresu.
Koda Sarkin Hadejia Buhari yayi shirinsa yayi Addu'ah sai ya Daga Kai sama. Sai Dan fatima ya zuba Kirari (Fasa maza dan Sambo, Garba Bakin Tandu da Man Madaci, wanda ake jira yazo, fasa Maza gagara gasa, sai ya buga Gangar yaki). Anan Mayakan Hadejia suka fara bugun mayakan Daular Sokoto suna kashewa. Wadansu duk suka razana suka fita a guje kowa yana kokarin ya ceci Ransa. Wadanda aka dauresu dan kar su shiga Hadejia da wuri, duk anan aka kashesu. Sauran kuwa suka zubar Makamansu suka Gudu. Dawakai suka Razana, su kuwa mayakan Hadejia Suna bi suna kashewa suna kama Bayi.

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...