Sunday, September 9, 2012

RUWAN DAMINA A HADEJIA



HADEJIA A YAU! Kamar yanda Aka sani Garin Hadejia Gari ne wanda Allah ya Albarkacemu da Ni'imomi da dama! musamman Kasar Noma da Ruwan kogi wanda kuma muke Alfahari da shi domin Noman Rani,Kifi, da kuma Dajin Kiwon Dabbobi da sauransu. Ko ban fada ba Tarihi ya Nuna cewa Hadejia ta kafu ne sakamakon Ruwa da ya wuce ta kasar Garin. shi kuma Ruwa yana tafe da Albarkatu da Dama kamar yanda na fada a baya! hasali ma Hadejia Ruwa ne ya kewayeta ta ko Ina. kuma muna Alfahari da hakan Saboda tattalin Arzikinmu. kamar yanda aka saba duk Shekara ana Samun Barazana Saboda Cikar Kogi da Gulbi da muke Dasu. A ranar Larabar nan Allah ya Ni'imtamu da Ruwan sama kamar da Bakin Kwarya. wanda kuma yayi Asarar Dukiyoyi da Gidaje da Dama. Muna Taya wadanda wannan Abu ya shafa jaje da kuma Addu'ar Allah ya Maida musu da Alkairi . AMEEN. kuma muna kara jawo Hankalin Mutanenmu da su rinka kula da tsaftace Magudanan Ruwa. sau da dama Idan Damina Ta wuce sai mu maida Magudanan Ruwanmu gurin zuba shara wanda kuma Hakan yana janyo mana Hasarar Gidaje da Dukiya! wani Lokaci ma Harda Rayuka. kowa ya gyara ya sani. Kuma muna kira ga Gwamnati da ta Rinka kula da kyautata Magudanan Ruwanmu, A matsayinta na Mai doka da Oda ko Ince wadda abin ya Shafa. Nasani tana Iya bakin kokarinta Domin mun samu labari wasu ma Tuni Gwamnati ta Jima da basu Sabon Matsuguni Amma Suka ki su tashi. Allah ya saka da Alkairi. Hadejia A yau.

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...