Wannan Dandali zai rinka kawo muku Labarai da suka shafi Gwamnatin Jihar Jigawa, da sauran muhimman labarai wadanda suka shafi rayuwar Al'ummah.
Thursday, June 14, 2012
JIHAR BORNO
MANYAN BORNO SUN ROKI DA A
KAWO KARSHEN RIKICIN BOKO
HARAM
HADEJIA A YAU! Al'ummar Jihar Borno dake
Arewacin Nigeria sun Roki 'yan kungiyar
Jama'atu Ahlussunna lidda'awati wal jihad
wadda aka fi sani da suna Boko Haram da
su Amince a tattauna dasu da Gwamnati
domin a kawo karshen Hare harenda yake
janyo Rasa rayuka da gidaje. A wata fira da
yayi da 'yan jarida a Maiduguri Dr. shettima
Ali Munguno ya bayyana rikicin boko haram
a matsayin rikici ne wanda ya janyo Asarar
rayukan Al'umma da gidaje, kuma ya janyo
Rashin aikin yi ga Al'umma. Ya bayyana
cewa mutane basu kwanciyar hankalin da
zasu tafiyar da rayuwarsu a tsinake, ko
harkokinsu na yau da kullum.uma ya
bayyana cewa Jama'a basu samun salloli
Biyar a cikin Jam'i saboda fargabar abinda
zai kasance,Saidai mutum yayi sallarsa a
cikin gidansa saboda rashin samun
nutsuwa. Dr.Ali Munguno ya kara da cewa
yana rokonsu da su Amince a tattauna dasu
domin a kawo karshen Asarar rayuka da
ake. yace a matsayinsu na 'yan kasa suna da
ikon rayuwa a jikin mutane ba tare da
tsangwama ba. yace duka mu da su
kasarmu ce, bamu da wata kasar da tafi
wannan. kuma ya kara da cewa Gwamnatin
tarayya tare da gwamnatin Jiha a hada
hannu wajen tattaunawar domin a kawo
karshen wannan Al'amari. http://
Isabohadejia.blogspot.com/
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar 1,HAUSAWA 2, ABORAWA (FULANI) 3, MANGAWA...
-
SARDAUNA/SHATIMA SUN KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI.... Daga Garba Tela Hadejia. A yau juma'a 29-5-2015 ne sabon zababben gwamnan jihar...
No comments:
Post a Comment
KA RUBUTA RA'AYINKA!