Friday, June 15, 2012

MAJALISSA TA DAKATAR DA HON.FARUK LAWAN

A yau juma'a ne majalissar Wakilan Nigeria tayi wani zaman Gaggawa inda ta Bayyana dakatar da Hon. Faruk Lawan A Mukaminsa na Shugaban kwamitin binciko badakalar rarar man fetur. wannan ya biyo baya ne Inda ake zarginsa da karbar Na goro kimanin Dala milyan dari uku. Kuma majalissar tuni ta maye gurbinsa da John Enoh mai wakiltar Obubra dake Jihar Cross River. Sannan majalissar ta umarci komitin ladabtarwa da ya hukunta Secretaren komitin wato Mr. Boniface Emalo wanda tuni shima aka rabashi da mukaminsa. kuma majalissar ta sake duba Matsayar da ta dauka a ranar 24 ga Afrilu na wanke kamfanin Zenon daga badakalar tallafin man. Inda kuma tana nan tana duba wannan batun.

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...