Wannan Dandali zai rinka kawo muku Labarai da suka shafi Gwamnatin Jihar Jigawa, da sauran muhimman labarai wadanda suka shafi rayuwar Al'ummah.
Thursday, June 14, 2012
TARIHIN SARKI HARU BUBBA
TARIHIN SARKIN HADEJIA HARU
BUBBA
Sarkin Hadeji Haru bubba shine Mahaifin
Sarkin Hadejia Muhammadu mai Shahada,
wanda a zamaninsa Turawa sukaci Hadejia
da yaki. Sarki Haru bubba Malami ne kuma
mutum ne mai son zaman lafiya, kuma shine
ya gina Masallacin juma'a Na Hadejia. Kuma a
zamaninsa Gumel sukayi yaki da Hadejia,
wato lokacin sarkin Gumel Abdu jatau.
Sarkin Gumel ya aikowa Sarkin Hadejia zai
wuce ta kasarsa wato ta kudu a gayawa
Talakawa kada su tsorata bazai taba kowa
ba. To amma koda yazo wucewa sai ya saba
Alkawari don yana sawa ana debe kayan
talakawan ana kaiwa Gumel. Koda Sarkin
Hadejia ya samu labari sai yasa akayi sirdi
aka fita, a wannan yakin aka kashe sarkin
Gumel Abdu jatau. Galadiman Hadejia
yakuba shine ya sareshi. Dama sarkin Gumel
yayi mafarki bazai koma gida ba. Sai ya
fadawa kaninsa Abubakar in ya mutu to a
kaishi Gumel ayi masa jana'iza, kuma hakan
akayi. Kuma a zamanin Sarkin Hadejia Haru
ne Dansa Muhammadu Yayi yaki da
Maguzawan Mada Rumfa ta Sokoto, inda
sarkin musulmi ya masa sarautar Sarkin
yakin Sarkin Musulmi. Kafin ya Zama Sarkin
Hadejia. Allah yaji kansu.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar 1,HAUSAWA 2, ABORAWA (FULANI) 3, MANGAWA...
-
SARDAUNA/SHATIMA SUN KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI.... Daga Garba Tela Hadejia. A yau juma'a 29-5-2015 ne sabon zababben gwamnan jihar...
No comments:
Post a Comment
KA RUBUTA RA'AYINKA!