Wannan Dandali zai rinka kawo muku Labarai da suka shafi Gwamnatin Jihar Jigawa, da sauran muhimman labarai wadanda suka shafi rayuwar Al'ummah.
Wednesday, June 13, 2012
TARIHIN SARAUTAR FULANI A
HADEJIA! A TAKAICE.
HADEJIA A YAU!
JIYA NA KAWO MUKU TAKAICACCEN TARIHIN
HADEJIA DA DALILIN KAFUWARTA.
TARIHIN FULANI- BISMILLAHIR-RAHMANIR-
RAHEEM.
Kamar yanda na fada a baya Sarkin Hadejia
Na sarakunan Habe shi ya nada Umaru a
matsayin sarkin fulanin Hadejia, To su fulani
sun taso ne daga Gabas da Machina akan
Hanyarsu ta yin kiwo, ko da sukazo Hadejia
sai suka tadda Garin akwai albarkar kiwo da
noma. Hakan ce tasa suka nemi izni a basu
gurinda zasu zauna A zamanin sarki
Abubakar Sarki na karshe a sarautar HABE.
Kuma suna tafe ne a karkashin jagorancin
HARDO ABDURE DAN JAMDOJI MACHINA. A
lokacin da Umaru yake a matsayin sarkin
fulanin Hadejia sai ya samu labarin jihadin
da SHEHU USMANU DAN FODIYO yakeyi hakan
tasa ya tashi 'yan-uwansa biyu(2) suje suyi
mubaya'a a gun SHEHU. Wato SAMBO DA
LARAIMA kuma hakan sukayi Inda shehu ya
basu Tutar jaddada Addinin Musulunci.
Kuma ya umarci SAMBO ya tsaya a HADEJIA
Shi kuma LARAIMA a MARMA. Saboda can
akwai dauloli suma masu zaman kansu yayi
kokarin Hadesu karkashin Daula guda daya.
kamar DAWA FAGI GATURWA DA MARMA. Shi
kuma SAMBO yaci gaba da jaddada Addinin
Musulunci a HADEJIA DA AUYO DA SAURAN
DAULOLIN SARAKUNAN HABE A karkashin
jagorancin Dan-uwansa Umaru. Bayan
rasuwar sarkin fulani Umaru SAMBO yaci
gaba da jaddada Addinin Musulunci har
saida suka kawar da SARAKUNAN HABE.
Amma ba yaki akayi ba Sai suka Koma Fantai
anan sukaci gaba da rayuwa. (wato akwai
wata tsangaya a kusa da gidan Labaran
fantai nan ne suka zauna) wadansu kuma
suka zauna a Dalla (akwai wata duriya a
dallah har zuwa Library anan suka zauna).
Sarakunan fulani sun karbi mulkin Kasar
Hadejia a karkashinDaular Usmaniyya.
ZAN KAWO MUKU TSARE TSAREN SARAUTA DA
KUMA HAKIMAN WAJEN KASAR HADEJIA A
LOKACIN SARKIN FULANIN HADEJIA MALAM
SAMBO. HADEJIA A YAU!
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...
-
HADEJIA A YAU! Kasar Hadejia tana da kabilu da dama wadanda kuma suke da yarensu daban-daban: kamar 1,HAUSAWA 2, ABORAWA (FULANI) 3, MANGAWA...
-
SARDAUNA/SHATIMA SUN KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI.... Daga Garba Tela Hadejia. A yau juma'a 29-5-2015 ne sabon zababben gwamnan jihar...
No comments:
Post a Comment
KA RUBUTA RA'AYINKA!