Monday, October 22, 2012

KWANAKIN HAJJI DA WURARE GOMA MASU ALBARKA. DAGA M. AMINU DAURAWA.

Easily Upload Your Images To Myspace
Free Music Hadejia a yau. Na daya ranar takwas ga watan hajji, sunanta
yaumuttarwiyya,
shine alhazai suke zuwa mina su wuni su kwana,
Na biyu ranar tara ga wata itace ranar arfa, itace
alhazai suke wuni a
filin arfa zuwa faduwar rana, daganan su tafi
Muzdalifa su kwana
Na uku ranar goma ga wata, itace alhazai suke
gabatar da aiyuka
guda biyar a cikinta, jifa, yanka, aski, dawafi, saayi,
Na hudu ranar sha daya , da sha biyu, da sha uku,
sune ranakun
kwanan mina da jifa, Abubuwa goma masu daraja a
Macca
wadanda suke da alaka da aikin hajji, wadanda ake
aiwatar da aikin
hajji, daura da su sune, na daya, Ka'aba ana kewaya
ta sau bakwai,
na biyu, alhiji (wanda ake cewa hijri isma'ila) ana
shiga ciki ayi
salla,daidai yake da yin sallah a cikin Ka'abah, na uku,
makamu
ibrahim, wanda ake sallah Raka'a biyu a bayansa
bayan gama
dawafi, na hudu, Alhajrul'aswad, (dutsen aljannah)
ana sunbatarsa
(kiss) a shefeshi, ayi sujjada akansa, ko anunashi daga
nesa ayi
kabbara, na biyar ruwan zamzam, ana sha a shafa a
fuska, a zuba
ajiki, ayi addu'a, aroki Allah bukarar duniya da lahira
hadisi ya
tabbata, akan haka, na shida Dutsen safa da marwa,
wanda ake
zirga-zirga tsakanin su sau bakwai a fara daga sama a
kare a marwa,
na takwas, mina wajen kwana da ranakun jifa, na tara
arfa da
muzdalifa, a wuni a arfa a kwana a muzdalifa, na
goma wajen jifa
guda uku, inda ake jefa tsakuwa guda saba'in, Allah
ta'ala yace
wanda ya girmama alamomin addinin Allah, yana
daga cikin tsoran
Allah na zuci, wanda duk yayi sallah a masallacin
macca yana da
lada dubu dari, wanda ladan ya shafi dukkan fadin
iyakokin harami,
tun daga ka'abah, Manzon Allah saw yace :Duk
wanda yayi hajji,
baiyi kwarkwasaba (maganar batsa da mata) baiyi
fasikanciba, zai
dawo kamar ranarda mahaifiyarsa ta haifeshi, kuma
yace, Hajji
kubutacce(shine wanda akayishi akan sunnah da iklasi
da ilmi) bashi
da sakamako sai aljannah, ku tayamu da addu'a mu
sami wannan
garabasar, Allah ya karbi ibadarmu yasa mu dace da
sunnah da
iklasi na gode

No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...