Tuesday, December 28, 2021

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..


Daga Nasiru Kainuwa Hadejia. 

Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a yammacin wannan rana. Wanda suka sami tarba da ga wajen shugaban Hadejia Ina Mafita Initiative Sir Baidi Gajo Elleman da mataimakinsa Dr Hussaini Shehu, sakataren ƙungiya Malam Salisu Muhamad Birniwa da sauran MEMBERS na ƙungiya.

Gamayyar ƙungiyoyin ta na wakiltar ƙungiyoyi sama da arba'in (40) na masarautar Ringim, ziyara ce ta sada zumunci tare da yabawa da irin aikace-aikacen da ina Mafita take aiwatarwa.

Gamayyar ƙungiyoyin sun yi jinjina haɗe da godiya ta musamma bisa yadda Ina Mafita ta zama silar samuwar wasu abubuwan alkhairi a  masarautarsu.

Shugaban Kungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative Sir Baidi Gajo Elleman. 

Wannan ziyara dai ba abin da take nunawa illa ƙaruwar samuwar danƙon zumunci a tsakanin masarautar Ringim da ta Hadejia wanda dama can haka abin yake mu na da kyakkyawar alaƙa a tsakaninmu. Wannan abin yabawa ne ace yau ƙungiyoyi su na tarayya a  wajen ciyar da jiharsu gaba bisa manufa guda.

Fatanmu a kullum Allah Ya ƙara haɗa kan al'ummar wannan jiha mai albarka, matsalolin da suka kewaye mu mu na roƙon Allah da ya kawo mana mafita.

Tuesday, November 30, 2021

AN GINA BURTSATSE GOMA A SASSAN HADEJIA..

 30 November 2021. 



Shugaban karamar hukumar hadejia Hon Abdulkadir Bala Umar T.O. Ya kammala aikin tona Sabbin Burtsatse (Tuka tuka) guda Goma a sassa daban daban na karamar Hukumar hadejia. 

Shugaban Karamar hukumar hadejia Honourable Bala Umar T.O. ya bayyana wannan aiki a matsayin wata hanya ce ta rage wahalar rashin ruwan sha a sassan da aka gina, sannan ya shawarci mazauna unguwannin da aka gina wannan Burtsatse da su rinka kula wajen sanarwa masu Unguwanni in ya lalace don gyarawa. 

Shugaban ya bayyana dalilin samo Wannan aikin a bisa kauracewa shiga karancin ruwa a wurare da dama na karamar hukumar, Kuma Alhamdulillah Masu unguwanni da wakilan Alumma da kungiyoyin Unguwanni sun nuna farin cikinsu da godiyarsu ga jajirtatten jagora A matsayin Shugaban karamar Hukuma. Tun zaman sa shugaban karamar hukumar Hadejia, Alhaji Bala Umar ya dukufa wajen inganta rayuwar Al'ummar wannan yanki, bayan ayyuka na raya karkara shugaban ya samar da wani tsari na tallafawa Mata masu kananan sana'oi wadda ake shirin kaddamarwa nan ba da jimawa ba. 

Daga karshe ya shawarci Alumma cewa suzama wakilan kansu wurin kula da wannan cigaba, yadda za'a jima Ana mora.


Daga Salisu Sogi Hadejia. 

Chairman Media Aide.

Monday, November 29, 2021

AN KADDAMAR DA GYARAN IDO KYAUTA A JIHAR JIGAWA...



Daga Garba Tela Hadejia... 

ƘUNGIYAR MATASA MUSULMAI TA DUNIYA DA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA HAƊIN GWIWAR GIDAUNIYAR MALAM INUWA SUN ƘADDAMAR DA AIKIN GYARAN IDO KYAUTA:-

A  satin da ya gabata, ɗumbin mutane masu fama da lalurar matsalar Ido kimanin mutum ɗari bakwai da ashirin da tara, (729) ne su ka amfana da samun aikin gyaran ido, da gilashin ƙara ƙarfin gani a fagen karatu, haɗi kuma da magungunan ciwon ido kyauta a Jihar Jigawa. 

Ƙungiyar musulmai matasa ta Duniya, da gwamnatin Jihar Jigawa, da haɗin gwiwar Gidauniyar ba da agaji ta Malam Inuwa, (Malm Inuwa Foundation) su ne su ka ɗaukin nauyin gudanar da aikin, su ka kuma ƙaddamar da shi a wannan rana a babbar Asibitin Kwanciya ta Haɗejia, (Haɗejia General Hospital), inda ɗumbin al'mma daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa su ka je aka yi musu aikin kyauta.

A cikin waɗannan jimillar mutanen kimanin (729), kimanin mutane hamsin ne aka yi wa aikin gyaran ido, aka kuma ba su magunguna kyauta, (Free Cataract Surgery, 50 Patient).

Sai kuma kimanin mutune ɗari biyu da ashirin da tara, waɗanda aka rabawa Gilashin ƙara ƙarfin gani domin samun damar karatu garau, (Free Dispensing Of Glasses, 229 Patient).

Sannan, kimanin mutum ɗari huɗu da hamsin ne aka rabawa magunguna kyauta bayan binciken likitoci ya tabbatar da matsalarsu ba ta gilashi ba ce, ba kuma ta aiki ba ce, magani kawai su ke buƙata lafiyar idonsu ta farfaɗo, 

(Free Drugs And Treatment, 450 Patients).

Ɗaya daga cikin marasa lafiyan da ya amfana da wannan aikin gyaran ido kyauta a zantawar da na yi da shi, ya shaida min cewa ya shafe tsawon shekara guda ya na fama da lalurar ido amma bai samu damar neman magani ba sai a wannan lokaci ya samu an yi masa aiki kyauta.

Ɗumbin marasa lafiyar da su ka amfana da wannan tallafi da al'umma gabaɗaya sun bayyana farin cikinsu da jin daɗinsu kan wannan aikin ido kyauta, sun kuma yi addu'ar fatan alkhairi ga wannan ƙungiya ta matasa musulmai ta duniya, da kuma gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI), da gidauniyar Malam Inuwa, da wanda ya assasa gidauniyar, mai girma shugaba hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) bisa wannan agaji da su ka yi. 

Aikin na gyaran ido kyauta wanda aka ƙaddamar da fara aiwatar da shi a yau, za a shafe tsawon kwanaki huɗu ana gudanar da shi, inda za a kammala a ranar Laraba, 24 ga wannan wata na Nuwamba, 2021. Insha Allah.



KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...