Monday, November 29, 2021

AN KADDAMAR DA GYARAN IDO KYAUTA A JIHAR JIGAWA...



Daga Garba Tela Hadejia... 

ƘUNGIYAR MATASA MUSULMAI TA DUNIYA DA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA HAƊIN GWIWAR GIDAUNIYAR MALAM INUWA SUN ƘADDAMAR DA AIKIN GYARAN IDO KYAUTA:-

A  satin da ya gabata, ɗumbin mutane masu fama da lalurar matsalar Ido kimanin mutum ɗari bakwai da ashirin da tara, (729) ne su ka amfana da samun aikin gyaran ido, da gilashin ƙara ƙarfin gani a fagen karatu, haɗi kuma da magungunan ciwon ido kyauta a Jihar Jigawa. 

Ƙungiyar musulmai matasa ta Duniya, da gwamnatin Jihar Jigawa, da haɗin gwiwar Gidauniyar ba da agaji ta Malam Inuwa, (Malm Inuwa Foundation) su ne su ka ɗaukin nauyin gudanar da aikin, su ka kuma ƙaddamar da shi a wannan rana a babbar Asibitin Kwanciya ta Haɗejia, (Haɗejia General Hospital), inda ɗumbin al'mma daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa su ka je aka yi musu aikin kyauta.

A cikin waɗannan jimillar mutanen kimanin (729), kimanin mutane hamsin ne aka yi wa aikin gyaran ido, aka kuma ba su magunguna kyauta, (Free Cataract Surgery, 50 Patient).

Sai kuma kimanin mutune ɗari biyu da ashirin da tara, waɗanda aka rabawa Gilashin ƙara ƙarfin gani domin samun damar karatu garau, (Free Dispensing Of Glasses, 229 Patient).

Sannan, kimanin mutum ɗari huɗu da hamsin ne aka rabawa magunguna kyauta bayan binciken likitoci ya tabbatar da matsalarsu ba ta gilashi ba ce, ba kuma ta aiki ba ce, magani kawai su ke buƙata lafiyar idonsu ta farfaɗo, 

(Free Drugs And Treatment, 450 Patients).

Ɗaya daga cikin marasa lafiyan da ya amfana da wannan aikin gyaran ido kyauta a zantawar da na yi da shi, ya shaida min cewa ya shafe tsawon shekara guda ya na fama da lalurar ido amma bai samu damar neman magani ba sai a wannan lokaci ya samu an yi masa aiki kyauta.

Ɗumbin marasa lafiyar da su ka amfana da wannan tallafi da al'umma gabaɗaya sun bayyana farin cikinsu da jin daɗinsu kan wannan aikin ido kyauta, sun kuma yi addu'ar fatan alkhairi ga wannan ƙungiya ta matasa musulmai ta duniya, da kuma gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, (MON, MNI), da gidauniyar Malam Inuwa, da wanda ya assasa gidauniyar, mai girma shugaba hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) bisa wannan agaji da su ka yi. 

Aikin na gyaran ido kyauta wanda aka ƙaddamar da fara aiwatar da shi a yau, za a shafe tsawon kwanaki huɗu ana gudanar da shi, inda za a kammala a ranar Laraba, 24 ga wannan wata na Nuwamba, 2021. Insha Allah.



No comments:

Post a Comment

KA RUBUTA RA'AYINKA!

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...