Saturday, May 30, 2015

AN KAMMALA TARON KADDAMAR DA KUNGIYAR MOVEMENT FOR THE RESTORATION OF NORTHERN NIGERIAN DIGINITY.


A Hadejia ta jihar jigawa ne aka kaddamar da wannan kungiya, a karkashin Jagorancin Dr. Aliyu M. Muri. na jami'ar umaru musa 'yar'adua dake katsina, taron ya sami halartar shugabanni da Membobi na kungiyar Muryar Talaka dake jihar jigawa, kuma an gabatar da Jawabai masu muhimmanci domin ganin an Taimakawa Gen. Buhari don ya Aiwatar da mulkinsa cikin Nasara. Da yake nasa Jawabin Dr. Aliyu Muri ya tabo fannoni da dama wanda jama'a zasu taimakawa kansu wajen zaben wanda zai wakilcesu a kowane mataki na Gwamnati, kuma yayi kira ga mahalarta taron dasu hada kai da hukumomin gwamnati domin samun nasara a duk harkokinsu na kungiya. Shima a nasa jawabin Comrade Bishir Dauda ya ja hankalin mahalarta taron wajen hada kai da hukumomi irin su NOA, EFCC, ICPC Da sauransu. Cikakken Rahoto zaizo daga Baya.

ZA'A KAI RUWA RANA TSAKANIN TSHOHON GWAMNAN JIGAWA SULE DA SABUWAR GWAMNATIN BADARU ABUBAKAR.


Alamu na nuna cewa a jahar jigawa za'akai Ruwa Rana Tsakanin tshohon Gwamnan jahar Sule lamido da kuma sabon Gwamna Alh Abubakar Talamiz Inda yanzu haka Sabon Gwamnan Alh Abubakar Badaru Ya musanta cewar: Tsahon Gwamnan Alh Sule lamido Sam Sam ba Biliyon Goma sha hudu 14n ya barmasa bashi ba ya ce kudin ya Nin ninka hakan Inda ya ce yanzu haka jahar ta jigawa ana binta kudaden da suka kama har kimanin Biliyon Dari da sha hudu 114b akasin abinda tsohon Gwamnan ya fadi a baya Dan haka sabon Gwamnan yayi alwashin yin bincike akan yadda aka bayar da duk basusukan. Shi kuma a nasa bangaren Shugaban Jam'iyar Adawa ta PDP a jahar Alh muhammed Mahamud Ku'it ya danganta wadannan maganganu da yan Jam'iyar ta APC sukeyi da cewar Jahilci ne ko kuma rashin sanin kwata kwata tsari na iya mulki. Sule lamido dai ya shafe shekaru takwas yana mulki a jihar jigawa, inda kuma yaci karensa babu babbaka sakamakon rashin 'yan Adawar da zasu taka masa birki game da yanda yake mulkin Jigawa. A satin da ya gabata ne Sule Lamidon ya tafi wani dogon hutu, inda ya bar Jihar a hannun sakataren Gwamnatin Jigawar wanda kuma shine ya mika mulki ga sabuwar Gwamnati, tuni dai masu sharhi suka danganta wancan hutu na Tsohon gwamnan da cewa wani salo ne na Tserewa sakamakon dinbin bashin da ya barwa Jihar. Abin jira a gani dai shine ko Sule Lamido zai dawo da wadannan kudade? Kokuma sai an kwatosu da karfi.

Friday, May 29, 2015

AN RANTSAR DA SABON GWAMNAN JIHAR JIGAWA. Daga Garba Tela Hadejia.


SARDAUNA/SHATIMA SUN KARBI RANTSUWAR KAMA AIKI.... Daga Garba Tela Hadejia. A yau juma'a 29-5-2015 ne sabon zababben gwamnan jihar Jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar (Sardaunan Ringim), da kuma mataimakinsa Barr. Ibrahim Hassan Hadejia (Shatiman Hadejia) suka karbi rantsuwar kama aiki gadan-gadan, domin hidima ga Al-ummar Jihar Jigawa. Da farko, an umarci Chief Jojin Jiha domin ya bude taro da Addu'a, Daga bisani, aka bukaci babban jigo a jam'iyyar ta (APC) wato Hon. Farouk Adamu Aliyu Birnin-Kudu ya gabatar da jawabinsa. Daga bisani aka sake bukatar Chief Jojin ya rantsar da mataimakin gwamna. Daganan kuma sai ya sake dawowa a karo na uku ya rantsar da gwamna.Bayan haka kuma aka Umarci mawaki Lawan Gujungu ya dan jijjiga-filin taro na wasu 'yan dakikoki kadan cikin sabuwar wakar da ya yiwa sabon gwamna. Daga bisani anso gabatar da Faretin girmamawa ga sabon Gwamna wanda jami'an tsaro za su gudanar amma hakan bata samuba sakamakon dandazon taron Al-umma masoya da suka cika filin wannan taro. Daganan kuma Sabon gwamna ya gabatar da jawabinsa ga Al-umma cikin harshen turanci bisa tanadin doka. A'karshe kuma, an gudanar da Addu'ar rufewa. Gami da 'yan shagulgula da jawabai kafin bajewa daga wannan filin taro. An gudanar da taron a filin taro na Malam Aminu Kano Tiraiangle dake birnin Jiha Dutse. Taron ya samu halattar dubban Al-umma daga sassa daban-daban na wannan Jiha. Sabon Gwamna da mataimakinsa, sunci alwashin gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci a wannan Jiha ta Jigawa. Insha Allah! A takaice, abin kenan da ya gudana ya yin rantsar da sabon zababben gwamnan Jihar Jigawa da mataimakinsa a birnin Jihar Jigawa Dutse. Muna kara godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana mai cike da farin ciki da tarihi a garemu. Allah ya taimakesu ya 'karfafesu akan dai-dai. Garba Tela Hadejia.

Thursday, May 14, 2015

YAN GUDUN HIJIRA....

YAN GUDUN HIJIRA!


Tun a lokacin da rikicin Boko Haram ya Addabi jihohin Borno da Yobe aka samu watsuwar 'yan gudun hijira a wasu sassa na Nigeria, ciki harda jihar Jigawa, kuma akasarin wadannan 'yan gudun hijira zakaga Mata ne da kankanan yara wadanda mafiya yawa suna a kasar Hadejia da kasar Gumel. A lokacin da suka fara zuwa wadannan yankuna saboda basu da abinda zasuyi dole wasu daga cikinsu suke bin masallatai da majlissai domin neman abinda zasuci abinci da yaransu. Abin tausayi zakaga yara da basu fi shekara 7 zuwa 10 ba suna bi kantuna da wurin zaman jama'a suna neman taimako. A kwanakin baya basuyi yawan da ya wuce kaga biyu ko uku ba a kullum amma yanzu abin sai karuwa yake wanda a kalla sai kaga goma zuwa sama a rana daya da mata da kananan yara abin tausayi, zaka gansu a kofar masallatai da kasuwa har da Bankuna wurin layin Atm. Dole mumini mai Imani ya tausayawa rayuwar wadannan bayin Allah domin ba a son ransu suka bar gidajensu da 'yan uwansu suka zo suke yin Bara ba! Saboda yawan kwararowarsu yasa jama'a sun fara kosawa ganin abin ya zama ba na kare ba, yanzu kullum a baka gansu a gidanka ba kaga biyar ko shida.

MASU HANNU DA SHUNI....

Hakika Masu hali sai sunyi amfani da damar da Allah ya basu wajen taimakon wadannnan bayin Allah da muhalli da Sutura da Abinci, da kuma kula da rayuwarsu musamman kananan yaran. yana da kyau masu hali su ware wani abu daga cikin Dukiyarsu don taimakon wadannan bayin Allah a matsayin Sadakatul-jariya.

GWAMNATI MAI JIRAN GADO...

Koda yake bani da masaniya game da yunkurin da Gwamnatin Jigawa tayi game da wadannan bayin Allah, kuma ban taba ganin wani wuri da aka ware don 'yan gudun hijira ba zanso in bada shawara ga Gwamnati mai jiran Gado, a karkashin jagorancin Jam'iyyar Apc, dasu fara duba wannan Matsalar ta 'yan Gudun Hijira kafin su fara Aiwatar da kowane Aiki domin ceto rayuwar wadannan Mata da kananan yara daga yin Bara, wanda hakan ya fara jefa wasu daga cikinsu zuwa ga halaka. An fara samun rade radin wadannan mata 'yan gudun hijira sun fara yin Arangama da wasu gurbatattun mutane suna yin lalata dasu suna basu kudi, har ma ance wasu da yawa sunyi cikin shege Allah ya kiyaye! Abin takaici sai kaga idan 'yan Hisbah suka kama mace tana lalata in suka bincika sai kaga 'yar gudun hijira ce. Kasan Dalilin da yasata cikin wannan hali?

SHAWARA GA GWAMNATI....

Ina bada shawara ga Gwamnati mai jiran gado da suyi la'akari da wannan matsalar domin su san ta yadda zasu bullowa wannan Al'amari, ya kamata Gwamnati ta samar musu mahalli na wucin gadi sannan ta sanya yaransu a Makaranta don ceto rayuwarsu. kuma Ina baiwa Gwamnati Shawara da ta sama musu sana'oi domin su dogara da kansu. misali Gwamnati zata iya amfani da makarantar koyon sana'a don koyawa Matan yanda ake yin SABULU, SAKA, DINKI,Da sauransu. Daga karshe ina Rokon Allah da kar ya nuna mana makamanciyar wannan Bala'i da zai sa mutum ya bar gidansa da iyalinsa ya tafi wani wuri yana yin abinda ko a Addini yana daga cikin Abu mai Kaskanci. Allah ka zaunar da kasarmu da Jiharmu lafiya.

Ismaila A Sabo Hadejia.
13/may/2015.

posted from Bloggeroid

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...