Thursday, June 4, 2015

YANDA DOLE TASA 'YAN GUDUN HIJIRA BARA A KASAR HADEJIA.

Tun daga lokacin da garin Allah zai waye har zuwa faduwar rana ka dinga cin karo kenan da Mata da Kananan yara suna yin bara ko naiman taimako, musamman a Arewa maso gabashin jihar Jigawa. Wadannan bayin Allah sun tsinci kansu a wannan hali ne sakamakon rikicin Boko Haram da ya Addabi Jihohin Borno da Yobe, dole wasu suka baro gidajensu domin neman tsira daga wannan Bala'i. Wasu kuma an kashe musu Mazajensu an kone gidajensu basu da wata sauran Dabara sai dai suyi bara domin su ciyar da kansu da yaransu.

Sakamakon Makwaftaka dake tsakaninsu da Jihar Jigawa, musamman Kasar Hadejia, bazakayi minti goma kana zaune ba sai kaci karo da wadannan bayin Allah suna cewa A taimaka mana da sadaka, mu 'yan gudun hijira ne..

A jihar Jigawa dai wadannan 'yan gudun hijira gwamnatin baya bata taba tallafa musu da komai ba, ko gida ko abinci ko sutura, sakamakon Kabilanci da yayi Tasiri a zuciyar tsohon gwamnan, wanda bincike ya nuna cewa abinda yasa ya nuna halin ko in kula ga wadannan mutane shine.. Suna zaune ne a wani bangaren Jihar ta Jigawa wanda kuma shi a zuciyarsa abin bai shafeshi ba.

Abin jira a gani dai shine... Ko sabuwar Gwamnatin Jigawa zata waiwaici wadannan bayin Allah? Ganin cewa wasu da yawa babu abinda zasu koma suyi a garuruwansu, sakamakon Kone musu gidaje da dukiyoyi da kashe musu 'yan-uwa da akayi. Allah ya baiwa sabuwar gwamnati ikon taimakawa......

http://bit.ly/K2WOg4

Monday, June 1, 2015

EFCC TA CAFKE MA'AIKATAN BUBBAN BANKI SU SHIDA.


DAGA JARIDAR LEADERSHIP. Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Nijeriya -EFCC za ta gurfanar da wasu manyan jami’an babban bankin kasar gaban kuliya bisa zargin yin zambar kusan naira biliyan takwas. Hukumar EFCC ta ce manyan jami’an bankin na CBN su shida tare da wasu jami’an bankunan ‘yan kasuwa na kasar su 16 sun hada baki wajen yin zambar wadannan makudan kudaden ta hanyar sauya adadin wasu tsofaffin kudi da suke kula da su.

A cikin wata sanarwa, kakakin EFCC Wilson Owujaren ya ce za a gurfanar da wadannan mutanen su 22 gaban babbar kotun tarayya da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo. A cewar EFCC jami’an na bankin CBN sun hada da Patience Okoro Eye, Afolabi Olufemi, Kolawole Babalola, Olaniran Muniru Adeola, Fatai Yusuf Adekunle da kuma Ilori Adekunle Sunday. Mazambatan suna yin wata badakala ce ta tsofaffi da kuma yagaggun kudade a jihohi da dama na kasar.

SABON GWAMNAN JIGAWA YA KAMA AIKI GADAN GADAN..


Sabuwar Gwamnati .... Kwana daya bayan rantsuwar Kama aiki Sabon Gwamnan Jihar Jigawa Alh. Badaru Abubakar ya kama aiki. In dai ba'a manta ba a ranar da aka rantsar da Sabon Gwamnan ya kai ziyara ga wasu wurare na gwamnatin domin farawa da Alkawurran da yayi ga 'yan Jigawa in suka zabeshi. Sabon Gwamnan kuma ya nada Sakataren Gwamnati wanda zai maye gurbin Lawal Abdu Babura, wanda aka nada shine Alh. Abdulkadir Fanini.

A bangare daya kuma sabon gwamnan ya bada sanarwar rushe Sakatarorin Karamar hukuma da Sakatarorin Ilmi na Jihar, kuma gwamnan ya bada sanarwar rushe duk wani mukami wanda siyasa ce ta nada shi. Jihar Jigawa tana daga cikin Jihohin da aka tafi aka bar mata bashin kudade, wanda kawo yanzu ana tunanin bashin ya doshi 114 billion. Abin jira a gani shine ko sabuwar gwamnati zatabi sawun wadannan kudade ko zata bari subi shanun sarki?

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...