Friday, June 15, 2012

MAJALISSA TA DAKATAR DA HON.FARUK LAWAN

A yau juma'a ne majalissar Wakilan Nigeria tayi wani zaman Gaggawa inda ta Bayyana dakatar da Hon. Faruk Lawan A Mukaminsa na Shugaban kwamitin binciko badakalar rarar man fetur. wannan ya biyo baya ne Inda ake zarginsa da karbar Na goro kimanin Dala milyan dari uku. Kuma majalissar tuni ta maye gurbinsa da John Enoh mai wakiltar Obubra dake Jihar Cross River. Sannan majalissar ta umarci komitin ladabtarwa da ya hukunta Secretaren komitin wato Mr. Boniface Emalo wanda tuni shima aka rabashi da mukaminsa. kuma majalissar ta sake duba Matsayar da ta dauka a ranar 24 ga Afrilu na wanke kamfanin Zenon daga badakalar tallafin man. Inda kuma tana nan tana duba wannan batun.

Thursday, June 14, 2012

JIHAR BORNO

MANYAN BORNO SUN ROKI DA A KAWO KARSHEN RIKICIN BOKO HARAM HADEJIA A YAU! Al'ummar Jihar Borno dake Arewacin Nigeria sun Roki 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunna lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram da su Amince a tattauna dasu da Gwamnati domin a kawo karshen Hare harenda yake janyo Rasa rayuka da gidaje. A wata fira da yayi da 'yan jarida a Maiduguri Dr. shettima Ali Munguno ya bayyana rikicin boko haram a matsayin rikici ne wanda ya janyo Asarar rayukan Al'umma da gidaje, kuma ya janyo Rashin aikin yi ga Al'umma. Ya bayyana cewa mutane basu kwanciyar hankalin da zasu tafiyar da rayuwarsu a tsinake, ko harkokinsu na yau da kullum.uma ya bayyana cewa Jama'a basu samun salloli Biyar a cikin Jam'i saboda fargabar abinda zai kasance,Saidai mutum yayi sallarsa a cikin gidansa saboda rashin samun nutsuwa. Dr.Ali Munguno ya kara da cewa yana rokonsu da su Amince a tattauna dasu domin a kawo karshen Asarar rayuka da ake. yace a matsayinsu na 'yan kasa suna da ikon rayuwa a jikin mutane ba tare da tsangwama ba. yace duka mu da su kasarmu ce, bamu da wata kasar da tafi wannan. kuma ya kara da cewa Gwamnatin tarayya tare da gwamnatin Jiha a hada hannu wajen tattaunawar domin a kawo karshen wannan Al'amari. http:// Isabohadejia.blogspot.com/

TARIHIN SARKI HARU BUBBA

TARIHIN SARKIN HADEJIA HARU BUBBA Sarkin Hadeji Haru bubba shine Mahaifin Sarkin Hadejia Muhammadu mai Shahada, wanda a zamaninsa Turawa sukaci Hadejia da yaki. Sarki Haru bubba Malami ne kuma mutum ne mai son zaman lafiya, kuma shine ya gina Masallacin juma'a Na Hadejia. Kuma a zamaninsa Gumel sukayi yaki da Hadejia, wato lokacin sarkin Gumel Abdu jatau. Sarkin Gumel ya aikowa Sarkin Hadejia zai wuce ta kasarsa wato ta kudu a gayawa Talakawa kada su tsorata bazai taba kowa ba. To amma koda yazo wucewa sai ya saba Alkawari don yana sawa ana debe kayan talakawan ana kaiwa Gumel. Koda Sarkin Hadejia ya samu labari sai yasa akayi sirdi aka fita, a wannan yakin aka kashe sarkin Gumel Abdu jatau. Galadiman Hadejia yakuba shine ya sareshi. Dama sarkin Gumel yayi mafarki bazai koma gida ba. Sai ya fadawa kaninsa Abubakar in ya mutu to a kaishi Gumel ayi masa jana'iza, kuma hakan akayi. Kuma a zamanin Sarkin Hadejia Haru ne Dansa Muhammadu Yayi yaki da Maguzawan Mada Rumfa ta Sokoto, inda sarkin musulmi ya masa sarautar Sarkin yakin Sarkin Musulmi. Kafin ya Zama Sarkin Hadejia. Allah yaji kansu.

Wednesday, June 13, 2012

TARIHIN SARAUTAR FULANI A HADEJIA! A TAKAICE. HADEJIA A YAU! JIYA NA KAWO MUKU TAKAICACCEN TARIHIN HADEJIA DA DALILIN KAFUWARTA. TARIHIN FULANI- BISMILLAHIR-RAHMANIR- RAHEEM. Kamar yanda na fada a baya Sarkin Hadejia Na sarakunan Habe shi ya nada Umaru a matsayin sarkin fulanin Hadejia, To su fulani sun taso ne daga Gabas da Machina akan Hanyarsu ta yin kiwo, ko da sukazo Hadejia sai suka tadda Garin akwai albarkar kiwo da noma. Hakan ce tasa suka nemi izni a basu gurinda zasu zauna A zamanin sarki Abubakar Sarki na karshe a sarautar HABE. Kuma suna tafe ne a karkashin jagorancin HARDO ABDURE DAN JAMDOJI MACHINA. A lokacin da Umaru yake a matsayin sarkin fulanin Hadejia sai ya samu labarin jihadin da SHEHU USMANU DAN FODIYO yakeyi hakan tasa ya tashi 'yan-uwansa biyu(2) suje suyi mubaya'a a gun SHEHU. Wato SAMBO DA LARAIMA kuma hakan sukayi Inda shehu ya basu Tutar jaddada Addinin Musulunci. Kuma ya umarci SAMBO ya tsaya a HADEJIA Shi kuma LARAIMA a MARMA. Saboda can akwai dauloli suma masu zaman kansu yayi kokarin Hadesu karkashin Daula guda daya. kamar DAWA FAGI GATURWA DA MARMA. Shi kuma SAMBO yaci gaba da jaddada Addinin Musulunci a HADEJIA DA AUYO DA SAURAN DAULOLIN SARAKUNAN HABE A karkashin jagorancin Dan-uwansa Umaru. Bayan rasuwar sarkin fulani Umaru SAMBO yaci gaba da jaddada Addinin Musulunci har saida suka kawar da SARAKUNAN HABE. Amma ba yaki akayi ba Sai suka Koma Fantai anan sukaci gaba da rayuwa. (wato akwai wata tsangaya a kusa da gidan Labaran fantai nan ne suka zauna) wadansu kuma suka zauna a Dalla (akwai wata duriya a dallah har zuwa Library anan suka zauna). Sarakunan fulani sun karbi mulkin Kasar Hadejia a karkashinDaular Usmaniyya. ZAN KAWO MUKU TSARE TSAREN SARAUTA DA KUMA HAKIMAN WAJEN KASAR HADEJIA A LOKACIN SARKIN FULANIN HADEJIA MALAM SAMBO. HADEJIA A YAU!
SARKIN MARMA MUHAMMADU DA MADARUMFA HADEJIA A YAU! Kamar yanda kuka gani A sama Zamu kawo muku Tarihin Zuwan Sarkin Marma Muhammadu Madarumfa. Iyakar sokoto da Niger da kuma yakin da akayi tsakanin Muhammadu da Tigarawan Madarumfa. akan kogin da ya raba Niger da Nigeria, kusa da Jibya. A zamanin Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Na Biyu. Kuma zamu baku tarihin Sarautarsa ta Sarkin yakin Sarkin Musulmi da kuma dawowarsa Hadejia da yanda aka kaiwa Sarkin Hadejia Haru Bubba Labarin Muhammadu. Harda Asalin Jafi da ake Ran sallah A kusa da Masallacin Juma'a. Muhammadu na Allah Ruwan kogi Tafi sannu sannu Wanda yayi wargi Ya Halaka. Giwa ta gama da Masu Karfi Ta wuce.
HADEJIA A YAU The Government and Society of Hadejia in the 19th Century: The government of Hadejia in the 19th century, like other emirates of the old Sokoto Caliphate, was based on autocracy. The emir who was a spiritual as well as temporal head was at the helm of affairs. He was assisted in governing by a class of officials or titleholders who were resident in his court. It was only the Sarkin Auyo who was permitted to stay outside the headquarters: he lived permanently at Auyo town. The composition of these titIe holders or Hakimai was made up of 'ya'yan Sarki (Princes), Dangin Sarki (emir's relatives), Barorin Sarki (clients), and Bayin Sarki (slaves). The structure of this emirate's administration was never dominated by the "Fulani ruling caste", since the heterogeneous nature of the area was taken into cognisance in the distribution of both civil and military offices. For example, during Sambo's reign the title of Madaki was held by a Bamange and that of Galadima was given to a Ba-Auyaki, both non-Fulani tribes. Militarily, the emir was the Commander-in- Chief of the emirate, delegating his function in practice to Sarkin Yaki (Captain General or War Chief), Jarma (Chief of the Brave Ones), Madaki, Sarkin Arewa and other war chiefs. The composition of the entire military force was made up of courtiers, title-holders and their household slaves, Dogarai (the emirate's bodyguards) and contingents from the "fiefs". Hadejia had two broad sectors of the army: the cavalry (Barade) and foot soldiers. Militarily the emirate was considered to be the strongest emirate east of Kano. This reputation it enjoyed and enhanced right from the days of the Buhari Revolt up to the coming of the British.

KUNGIYAR HADEJIA INA MAFITA TA KARBI BAKUNCIN KUNGIYAR JIGAWA NORTON WEST..

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia.  Ziyarar wakilai da ga gamayyar ƙungiyoyin masarautar Ringim, zuwa ga ƙungiyar Hadejia Ina Mafita Initiative a ...